3 Yuni 2021 - 13:05
Kungiyar Kwadago Ta Duniya: Mutane Miliyan 75 Za Su Rasa Aikin Yi A Duniya

Kungiyar kwadagon ta duniya ta sanar a jiya Laraba cewa; Cutar Cuvid-19 wacce ta fara yaduwa a duniya tun watanni 17 da su ka gabata,ta jefa ma’aiakta miliyan 100 a cikin talauci saboda raguwar sa’o’in yin aiki da kuma rashin samun damar wasu ayyukan.

ABNA24 : Kungiyar ta kwadago ta kuma yi gargadin cewa; Matsalar da ake ciki za ta tsawaita kuma yanayin aiki da bai koma kamar yadda ake gabanin bullar cutar annobar ba, har sai an shiga shekarar 2023.

Dangane da wannan shekarar da ake ciki kuwa, rahoton na kungiyar kwadago ya ce; A shekarar da ake ciki mutane miliyan 75 ne za su rasa ayyukansu.

342/